Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi reshen jihar Katsina Kwamred Nasiru Wada Mai’adua ya yi wannan kira a wata takardar sanar wa da aka rabawa manema labarai.
Ya ce a wannan wata mai daraja ya zama wajibi masu hali su fito su tallafawa marayu, masu buƙatar na musamman da marasa ƙarfi.
“Ya zama wajibi mu fito mu tallafa wa waɗannan mabuƙata da kayan abinci, kuɗi da sutura domin suma su sami natsuwa wajen gudanar azumin watan Ramadan”,inji shugaban NULGE.
Kwamred Wada Mai’adua ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da yan majalisu na ƙasa da shugaban ƙananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati da suka fara raba tallafi na kuɗi da kayan masarufi ga al’ummar saɓanin azumi.
Yayi kira ga masu hali a jihar da su bi sahun waɗannan shugabanni wajen raba irin wannan tallafi da yace Allah zai mai da masu da abinda ya fi haka.
Haka kuma ya jawo hankalin wasu ‘yan kasuwa da ke ƙara farashin kayan masarufi da sauran kayan buƙata a wannan wata mai tsarki da su tsoron Allah su dai na.
Shugaban ƙungiyar ya danganta bala’o’in da ke addabar yankin da halayen irin waɗannan yan kasuwa.
Kwamred Nasiru Wada ya kuma jajantawa ‘yan kasuwan Kano kan iftala’in gobara da ya shafa da fatan Allah mayar masu da abinda yafi haka.
