Jami’an EFCC sun tsare El-Rufa’i a ofishinsu har dare yayin bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya kasance a halin bincike har zuwa daren Litinin wayewar Talata a komar Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a Abuja, sa’o’i bayan amsa gayyatarta.

A lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an EFCCn ko makusantan El-Rufai ba su bayar da ba’asi akan adadin lokacin da zai ɗauka a hannun Hukumar ba.

Tun da safiyar Litinin ɗin ne El-Rufa’i ya je ofishin hukumar da ke yankin Jabi a birnin tarayyar, kamar yadda mai taimaka masa akan lamuran labarai Muyiwa Adekeye ya shaida ta wani saƙo a kafar X.

An ga yadda aka ƙarfafa tsaro yayin da magoya baya da masu sukar tsohon gwamnan suka yi cincirindo a wajen hedikwatar hukumar.

Wannan al’amari ya haifar da zanga-zanga tsakanin ɓangarorin biyu wajen bayyana mabanbanta ra’ayoyinsu akan El-Rufa’in.

A yayin haka ne wani ɗan ɓangaren adawa da El-Rufa’i mai suna Muhammad Abdullahi ya ce binciken rashawa da ake masa na bisa doka don haka kada a yi ƙoƙarin siyasantar da shi.

By Babaji