Gobarar Singa: Gwamnatin Tarayya ta tallafa da biliyan N5 yayin da Shettima ya jagoranci yunƙurin rage raɗaɗi

Spread the love
Screenshot

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima, ya wakilci Shugaban Ƙasa domin jajenta wa al’ummar Jihar Kano musamman ‘yan kasuwar Singa bisa iftila’in gobarar da ta afka musu tare da haddasa asarar dukiya mai yawa.

Ziyarar ta gudana ne tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa kasuwar domin duba irin ɓarnar da gobarar ta yi da kuma jajenta wa waɗanda abin ya shafa.

A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana matuƙar kaɗuwa da damuwa akan wannan mummunan lamari, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta tsaya tsayin daka wajen tallafa wa ‘yan kasuwar da suka yi asara.

Haka kuma, ya sanar da ware Naira biliyan biyar a matsayin tallafin gaggawa domin farfaɗo da harkokin kasuwanci da rage raɗaɗin asarar da aka yi.

Shettima ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da ta Jihar Kano zai ƙara ƙarfi wajen ganin an samar da mafita mai ɗorewa a game aukuwar ire-iren iftila’in.

Sannan, ya bayyana cewa za a samar da matakan ɗaukar kariya domin kauce wa faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

By Babaji