Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
An samu ɓarkewar rikici a Madobi bayan da aka fara shirye-shiryen naɗa sabon Dagacin Madobi sakamakon rasuwar tsohon dagacin, Alhaji Umaru Mahmud.
Rikicin ya samo asali ne bayan wasu daga cikin masu neman kujerar dagacin sun kalubalanci tsarin da suka ce Hakimin Madobi, Alhaji Saleh Musa Saleh, ya bi wajen zaben sabon dagacin.
ɗaya daga cikin masu neman kujerar, Tafidan Madobi, Alhaji Hussain Sarki Aliyu Rabakaya, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda aka gudanar da tsarin zaben. Ya ce ba a bi ƙa’idojin al’ada da tsarin da aka saba amfani da su ba wajen zaɓar wanda zai gaji marigayi dagacin.
Alhaji Hussain, wanda Dakta Usman Sarki Sulaiman ya wakilta, ya jaddada cewa ba za su amince da tsarin da aka bi ba, yana mai zargin cewa an cire sunayen wasu daga cikin masu neman kujerar tare da sanya wasu da ba su dace da tsarin ba.
Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, Hakimin Madobi, Alhaji Saleh Musa Saleh, bai fitar da wata sanarwa ko ƙarin bayani ba dangane da zarge-zargen da ake yi masa.
