Gombe: Ɗan Majalisar Wakilai, Garba ya koma APC daga PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karɓi baƙuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu-Deba, Hon. Inuwa Garba, zuwa cikin Jam’iyyar APC bayan sauya sheƙarsa daga PDP.

A lokacin ziyarar, Hon. Garba ya gabatar wa gwamnan katinsa na shaidar zama ɗan jam’iyyar APC a hukumance, wanda ya yanka daga Gundumarsa ta Luɓo a Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba, wanda ke nuna tabbacin komawarsa jam’iyyar mai mulki.

A cewar ɗan majalisar, ya samu ƙwarin-gwiwa ne daga kyakkyawan jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya bisa kyawawan manufofinsa da suka shafi jama’a, da kuma ɗimbin ayyukan da ya yi a faɗin Jihar Gombe, da kuma kyakkyawan shirin Sabunta Fata na Shugaba Bola Tinubu, kamar yadda Daraktan yaɗa labaran gwamma, Ismaila Uba Misilli ya bayyana a wata takarda.

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa, APC tana bada wata dama mai muhimmanci, kwanciyar hankali da ci-gaba, mai ɗorewa, da shugabancin dake damawa da kowa da kuma arziƙi mai ɗorewa ga al’ummar ƙasa.

Haka kuma, ya yi alƙawarin cikakkiyar biyayya da jajircewarsa ga jam’iyyar da shugabanninta domin cimma nasarori yayin kasancewar sa acikinta.

A nasa jawabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da ɗan majalisar zuwa APC, inda ya yaba wa jajircewarsa da kuma yadda yake sauƙe nauyin da ke kansa na al’ummar mazaɓarsa.

Ya bayyana sauya sheƙar a matsayin goyon baya mai ƙarfi ga jam’iyyar a Gombe, da kuma ƙarin tabbaci na tsarin shugabancin gwamnati mai mayar da hankali kan ci-gaban al’umma.

By Babaji