
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai tare ‘yan bijilante da mafarauta, sun yi nasarar halaka babban Kwamandan Boko Haram da kama wani da ake zargin sa da yi wa mayaƙansu safarar kayan aiki a Ƙaramar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa.
A cewar majiyoyin tsaro kamar yadda masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya ruwaito, an ƙaddamar da atisayen farkon ne a ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
An ruwaito cewa sojojin sun yi arangama ne da mayaƙan a wani yanki na Visik River line. A yayin ba-takashi a tsakaninsu ne aka halaka Abdullahi Mafa, wanda kwamandan Boko Haram ne a yankin Madagali.
Bayan sa’a guda ne dakarun suka garzaya tashar mota ta Madagali, inda suka yi nasarar kama wani ɗan shekara 64 mai suna Dauda Usman Gubula. Ana zargin sa da yi wa mayaƙan safarar kayan yaƙi da wasu ababe domin taimaka wa ayyukansu.
Jami’an tsaro sun ce, an kuma ƙwato jirage marasa matuƙa biyu da na’urorin caji masu amfani da hasken rana guda 20.
A yanzu haka dai an tsare shi yayin da ake cigaba da gudanar da bincike akansa domin samo ƙarin wasu bayanai.
Haka na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun suke ƙara ƙaimi wajen daƙile ayyukan Boko Haram da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Gabashin Nijeriya.


