Shaguna sama da 50 sun ƙone a wata gobara a kasuwar Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar yau Juma’a ne aka sake samun iftila’in gobara a wata kasuwar Jihar Kano, wadda ta yi sanadin ƙone akalla shaguna sama da hamsin.

Al’amarin ya auku ne a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose da ke yankin Dakata a birnin Kano.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 5:40 na asuba, inda wutar ta cigaba da ƙone shaguna har zuwa wayewar garin kana jami’an hukumar kashe gobara suka isa wajen domin shawo kan al’amarin.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce, tana gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar gobarar da kuma tantance adadin shagunan da ta shafa.

A cewar Shugaban kwamitin gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, al’amarin ya jefa firgici acikin al’umma Musa ganin yadda gobarar da cigaba da ruruwa har zuwa safiya.

Ya bayyana cewa, iftila’in ya shafi galibi shagunan da ke samar da mai da kayayyakin da suka shafin leda, waɗanda sun taimaka wajen haɓaka ɓarnar gobarar.

A halin yanzu babu wani cikakken bayani game da abin da ya haddasa gobarar ba, sannan babu rahoton mutuwa, sai dai hasarar da ‘yan kasuwa suka tafka.

By Babaji