
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin farin kaya DSS, ta sake buɗe bincike akan batun ɓacewar Abubakar Idris a 2019, wanda aka fi sani da Dadiyata, tare da shirin gayyatar wasu da ake zargi domin amsa tambayoyi a kai bayan kusan shekaru bakwai da faruwar al’amarin.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa hukumar ta gayyaci waɗansu mutane da aka alaƙanta su da al’amarin domin su bayar da ba’asin abin da suka sani a kai.
Dadiyata, malami ne a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina, wanda ya ɓace ne tun a ranar 2 ga watan Agustan 2019 bayan wasu ‘yan bindiga sun sace shi daga gidansa da ke yankin Barnawa a Kaduna. Tun daga lokacin har yanzu ba a san inda yake ba.
An sake buɗe batun ne a daidai lokacin al’umma suak karkata hankali akan kalaman tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da kuma kokawa cikin tausayi daga ɓangaren matarsa, Kadijah a wani faifan bidiyo.
Reno Omokri, wanda tsohon mataimaki ne ga shugaban ƙasa, ya wallafa bidiyon a shafinsa na X, inda aka ga matar Dadiyata na bayyana sabon damuwa kan ɓacewar mijin nata.
Omokri ya kai mata ziyara a gidanta tare da yin kira ga jama’a da su tallafa mata da ‘ya’yanta, yana mai alƙawarin neman adalci a akan lamarin a matsayin wani ɓangare na lallashin iyalansa.
A cewarsa matar, an sace Dadiyata ne yayin da yake sauka daga motarsa a harabar gidansu a ranar 2 ga Agustan 2019, inda ta ce ta ga abin da ya faru daga taga.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu wani jawabi a hukumance ba daga DSS akan dalilan sake buɗe binciken ba ko kuma akan waɗanda aka gayyata.
