Sarki Charles na Birtaniya ya magantu kan kama ɗan uwansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Birtaniya, Charles na III ya ce wajibi ne a bar doka ta yi aikinta bayan ‘yan sanda sun kama ɗan uwansa, Andrew Mountbatten-Windsor bisa zargin sa da rashin kiyaye dokokin aikin gwamnati.

A wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar a ranar Alhamis, Sarkin ya ce abin da ya rage yanzu shine a gudanar da bincike akan al’amarin bisa gaskiya da adalci, yana mai cewa za su bayar da cikakken goyon baya a yayin haka.

Ya jaddada cewa, shi da iyalansa za su cigaba da aikinsu da yi wa al’umma hidima yadda ya dace.

Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan sandan Thames Valley suka tabbatar da kamen da kuma yin bincike a wasu adireshi biyu masu alaƙa da Andrew.

A yayin haka ne aka kama wani ɗan kimanin shekaru 60 a yankin Norfolk, wanda a yanzu yake hannun ‘yan sanda da ke cigaba da gudanar da bincike akansa.

Duk da cewa ba a bayyana dalilan kamen ba, ‘yan sandan Thames Valley sun ce suna bincike akan ikirarin cewa Andrew mai shekaru 65 a lokacin da yake riƙe da muƙamin jakadan kasuwanci, ya fitar da wasu bayanan gwamnati na sirri ga marigayi Jeffrey Epstein da aka ai aiwatar wa hukunci akan laifin cin zarafi.

By Babaji