Victor Font ya alƙawarta dawo da Lionel Messi Barcelona idan aka zaɓe shi shugaba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Victor Font ya jaddada aniyarsa ta dawo da Lionel Messi ƙungiyar Barcelona, inda ya ce ɗan Ajantinar ya cancanci samun bankawa mai cike da tsari a filin Camp Nou.

A shekarar 2021 ne Messi ya bar Barcelona bayan da ƙungiyar ta gaza sabunta zamansa saboda ƙalubalen kuɗaɗe da ta fuskanta.

Ganin haka ya sa zakaran ɗan ƙwallon duniyar ya koma Paris Saint-Germain, inda kuma daga bisani ya koma Inter Miami a Amurka da ke buga Gasar Major League Soccer.

Duk da cewa ya bar Barcelona, Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas, an yi ta kwaɗayin ya koma taka leda a ƙungiyar saboda muhimmiyar rawa da ake fatan zai taka wajen ci-gaban ƙungiyar.

A cewar Font, wanda ɗaya ne daga cikin ‘yan takarar shugabancin Barcelona ta wata hira da jaridar AS, yana fatan dawo da Lionel Messi cikin ƙungiyar muddin ya zama shugaba.

Ya yaba wa Messi akan nasarorinsa a wasanni da kuma abin da ya wakilci magoya bayan Barcelona akansu na ɗaga darajar ƙungiyar.

Font ya ƙara da cewa, lallai bai wadatar a ce Messi ya yi wa ‘yan Barcelona bankawa ta bayan fage ba kaɗai, don haka ya dace ya yi murabus a ƙungiyar.

Kazalika, ya ce za su ba Messi matsayi na dogon zango a ƙungiyar ta yadda zai riƙe hatta shugabancin kulob ɗin.

By Babaji