An tasa ƙeyar tsofaffin jami’an RTEAN biyu kurkuku kan bijire wa umarnin kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zaune a Abuja ta umarci a garzaya da tsofaffin jami’an Ƙungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Ƙasa (RTEAN) zuwa gidan yarin Kuje da ke Babban Birnin Tarayyar.

Mai Shari’a O.Y. Anuwe yayin hukuncin, wanda aka yi a ranar Talata, ya ce an samu Mista Eriyo Osakpamwan da Yusuf Ibrahim Adeniyi da laifin raina hukuncin kotun da bijire masa, wanda ta yi a ranar 13 ga watan Oktoban 2020.

Osakpamwan ya yi ikirarin zama Shugaban RTEAN yayin da Adeniyi ya riƙe muƙamin Sakatare Janar na ƙungiyar har zuwa 2025 a lokacin da aka sallame shi bisa zargin sa da laifukan saɓa wa dokokin aiki da cin amana.

Tuni dai kotun ta bayar da izinin a kama su kuma a tsare su har sai sun wanke kansu ta hanyar gabatar da takardar rantsuwa akan tabbatar da bin umarnin kotun.

An fara shari’ar ne tun a rikicin shugabancin RTEAN da aka faro a 2019. A watan Oktoban 2020 kotun ta yi hukuncin soke halascin shugabancin Osakpamwan a RTEAN, inda ta kuma haramta masa ikirarin shi shugaban ƙungiyar ne.

Haka kuma, ta soke dukkan hukuncin da ya ɗauka yayin zama shugaban da umartar sa da ya fice daga ofishin ƙungiyar na Abuja.

Duk da cewa ya ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara a shekarar 2021, hakan bai sa ya yi nasara ba domin ita ma ta yi watsi da batun sakamakon rashin nagarta.

Daga bisani ya cigaba da ikirarin cewa shi ne sahihin shugaban RTEAN, inda waɗanda suka shigar da ƙarar, suka gabatar da shaida akan haka duk da umarnin kotun.

By Babaji