Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana alhinin sa kan rasuwar fitaccen marubuci kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Bello Musa Ɗankano.
Ɗankano, mai shekaru 71, ya rasu ne a ranar Lahadi a Katsina.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗa na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar jama’a da kuma bunƙasa adabi.
“Bello Musa Ɗankano ba kawai marubuci ba ne; mai bayar da labari ne wanda ya yi amfani da adabi a matsayin hanyar bayyana gaskiya, darussa na ɗabi’a da sauyin al’umma. Rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Katsina da al’ummar marubuta na Nigeriya,” in ji Dikko.
Ya ƙara da cewa aikinsa a gwamnati da kuma rubuce-rubuce da yayi ya samar da gagarumar gudunmawa ga harkokin mulki da adabin Arewacin Najeriya.
Ya riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, kwamishinan yaɗa labarai, harkokin cikin gida da al’adu, sannan ya kasance marubucin jawabai ga gwamnonin da suka gabata.
Fahimtarsa a fannin mulki ta ƙara armashi ga ayyukansa na adabi, inda suka zama madubi na halin da al’umma ke ciki,” in ji Raɗɗa.
Gwamnan ya bayyana muhimmancin fitattun littattafan marigayin, da suka haɗa da A Season of Locusts, Petrol Station, My Cousins and I, da The Last Caravan da wasu gajeren labarai, yana mai cewa sun taka rawa wajen bunƙasa adabin Najeriya.
Gwamna Raɗɗa ya kuma miƙa ta’aziyya ta musamman ga Hakimin Malumfashi kuma Galadiman Katsina, Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta, da iyalan sarauta da ɗaukacin al’ummar Malumfashi.
Ya yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya gafarta masa, ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa, tare da bai wa iyalansa, al’ummar Malumfashi da ɗaukacin al’ummar marubuta juriyar jure wannan rashi.
