Daga SANUSI MUHAMMAD a Sokoto
Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar hukumar bada ilimi bai ɗaya ta jihar Sokoto sun gudanar da wani taron tattaunawa na kwana biyu kan wayar da kan jama’a da kafofin watsa labarai don ƙarfafa Ilimin ƙananan yara a matakin farko (ECCE) da kuma haɓaka samun ingantaccen ilimi a Jihohin Sokoto, Kebbi, da Zamfara.
A cikin saƙonsa babban ofishin kula da UNICEF, reshen Jihar Sokoto, Dr. Michael Juma ya ce, tattaunawar da kafofin watsa labarai an shiyar shi ne don wayar da kan jama’a kan manufofi, don cigaban ilimin yara.
Dr. Michael Juma ya bayyana cewa manufofin taron bitar shine tabbatar da cewa kowane yaro, ba tare da la’akari da asalinsa ba, yana da daidaito wajen samun ingantaccen ilimi (ECCE), yana mai cewa shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin UNICEF na tallafawa burin gwamnatin Najeriya don samun ingantaccen ilimi ga dukkan yara.
A cikin wani saƙon fatan alheri, sakataren dindindin na ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Sokoto, Alh. Sanusi Binji ya ce, tsarin Ilimi na ECCE na da matuƙar muhimmanci ga ilmantarwa ga ƙananan yara.
A cewarsa, gwamnati, da abokan hulɗar ci gaba irin su UNICEF, kafofin watsa labarai, da al’ummomi dole ne su yi aiki tare don cimma burin ECCE a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.
Ya kuma ambaci cewa ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Sokoto ta ƙuduri aniyar tallafawa yaƙin wayar da kan jama’a kan muhimmancin ECCE.
Ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su samar da dabarun aiki don faɗaɗa ilimi, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa don bunƙasa tsarin Ilimi na ECCE.
Alh. Sanusi Binji ya ba da shawarar cewa gwamnatocin jihohi uku na Sokoto, Kebbi da Zamfara dole ne su samar da dabarun aiki don inganta ilimi, amfani da kafofin watsa labarai don fafutukar kare haƙƙin jama’a da kuma tabbatar da cewar tsarin Ilimi na ECCE ya isa kowane lungu na jihohin.
