Abnur Entertainment ya dakatar da ayyuka kan rasuwar Nura Shariff

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanonin shirya finafinai na Abnur Entertainment da General Media Solutions da ke Kano sun sanar da dakatar da gudanar da ayyukansu bisa rasuwar ɗaya daga cikin ma’aikatansu, Nura Shariff.

Sun yanke ɗaukar matakin ne domin nuna alhininsu game da rashin ma’aikatacin wanday a kasance amintacce, gogagge, mai ƙwazo akan aikinsa kuma na gari.

Akan haka ne suka ɗauki matakai kamar haka: Ofishin Abnur da ke Kano za a rufe shi har zuwa kammala addu’ar kwanaki bakwai.

Sannan, dukkan ayyukan fita waje (shooting), tallace-tallace (advertorial activities), da kuma duk wani film da ake nunawa a halin yanzu, za a dakatar da su har zuwa bayan addu’ar kwanaki 40.

Haka kuma, duk wani shiri da aka tsara za a dawo da shi ko a fara nunawa, za a ɗage shi har sai bayan kwanaki 40.

A cewarsu, an ɗauki matakan ne domin girmama marigayin da kuma ba wa ma’aikata da abokan hulɗa damar alhinin wannan babban rashi, kamar yadda suka bayyana a wata takarda da Amina Adam da Abdul Amart na Abnur suka fitar ta bayyana.

A ƙarshe, sun yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalai da abokan aiki haƙurin jure rashin sa.

By Babaji