
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin Majalisar Dattawa akan Kuɗaɗe, ya bayar da izinin kama babban rajistiran Hukumar kula da Lamuran Rajistar Harkokin Kasuwanci (CAC), Hussaini Ishaq Magaji bisa zargin sa da ƙin amsa gayyatar da majalisar da sha yi masa a baya.
Kwamitin ya bada izinin ne a ranar Alhamis yayin zama akan kare kasafi da ya ƙunshi Ma’aikatar Kuɗi da hukumomin da ke ƙarƙashinta.
Shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa ya zargi Ishaq Magaji da ƙin biyayya ga kwamitin da gangan.
Ya ce, ana gayyatar sa ne domin ya zo ya fayyace matsalolin da suka shafi lamuran kuɗaɗe a hukumar ta CAC.
“Muna da matsalolin da suka shafi daidaiton kuɗaɗen shiga na CAC, amma duk sadda muka gayyace shi, sai ya turo wani jami’i na ƙasa da shi”, inji Sanata Musa.
Sanata Orji Uzor Kalu, wanda shi ma mamba ne a kwamitin, shi ne wanda ya fara gabatar da batu akan rajistiran, inda ya roƙi kwamitin da ya nemi a kai ƙorafinsa ga Shugaba Bola Tinubu domin ya tsige shi a muƙamin.
Haka ma, Adamsa Oshiomhole na kwamitin, wanda ya ce akwai buƙatar kada kwamitin ya amince da kowane irin kasafi da aka ware wa hukumar a dokar kasafin 2026 har sai Magaji ya hallara a gaban kwamitin, shawarar da shugabancin kwamitin ya amince da ita.
