
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyun adawa a Nijeriya, sun yi watsi da sabuwar dokar zaɓe ta 2026 da aka yi wa gyaran fuska a kwanan nan da majalisar dokokin ƙasar da tabbatar kuma Shugaba Bola Tinubu ya amince da ita a hukumance.
Sun yi kira ga majalisar dokokin da ta gaggauta shirin sake sabon gyara akan kundin dokar tare da cire dukkan hukunce-hukuncen da suka janyo cece-kuce acikin al’umma.
Jam’iyyun sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka yi wa laƙabi da ‘kiran gaggawa don ceto dimukraɗiyyar Nijeriya” da kaz yi a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Alhamis.
A wata takarda da Shugaban Jam’iyyar NNPP, Ahmed Ajuji ya fitar, jagororin adawar sun nemi Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta fara shirye-shiryen kwaskwarima ga kundin dokokin zaɓen na 2026 tare da cire dukkan sashen da suka janyo rashin amincewar ‘yan ƙasa da tabbatar wuraren da al’umma suka gamsu da su don tabbatarda gaskiya da adalcin zaɓuka.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun haɗa da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark; tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola; tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi, waɗanda dukkan su ‘yan Jam’iyyar ADC ne.
Haka kuma taron ya samu halartar Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ahmed Ajuji da wasu sanannun ‘yan jam’iyyar kamar su Buba Galadima.
