‘Ba ni da bindiga’: Tinubu kan zargin sa da kassara ɓangaren adawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da ikirarin cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin kassara jam’iyyun adawa, yana mai cewa ba yi amfani da ikon mulki ba wajen tursasawa wajen barin jam’iyya ga ‘yan siyasa ko rufe bakin ‘yan adawa.

Tinubu ya bayyana haka ne a yayin liyafar buɗe baki na musulmi da kirista da ya ƙunshi sanatoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ƙasar ya yi tsokacin ne a lokacin yake bada amsa game da sukar Jam’iyya mai mulki (APC) akan ƙara ƙarfi da hanyar zargin tursasawa ‘yan adawa komawa cikinta.

“Lallai ne masu suka sai sun yi magana a sa’ilin da suke zargi na da kashe ‘yan adawa, saidai ba ni da bindiga. Da zan bai wa kaina lasisi idan ina da ikon”, inji Tinubu.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan siyasa suke tururuwar shiga APC, lamarin da ya haddasa cece-kuce zargi sauya yanayin siyasar Nijeriya daga ɓangaren jam’iya mai mulki.

Tuni dai shugaban ƙasar ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya ce ‘yan majalisu da sauran ‘yan siyasa suna yin haka ne don raɗin kansu ba ƙarƙashin tilastawa ba.

Kazalika, Tinubu ya yi tsokaci akan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta musamman a lamuran tsaro da ya shafi harkokin siyasa da zamantakewar al’umma, yana mai kira ga haɗin kai tsakanin jagororin siyasa a madadin rikici akan wasu ababen da ka iya haddasa koma-baya ga ci-gaban ƙasa.

By Babaji