
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Juma’a Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwa game da faɗaɗar ayyukan ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Alƙaleri da ke Jihar Bauchi, inda ya yi gargaɗin cewa matakin da al’amarin yake a yanzu ka iya haddasa babbar fitina matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa a kai ba.
Bala Mohammed ya bayyana haka ne bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya bai wa shugaban ƙasar ba’asin halin tsaro a sassan jihar tasa.
Da yake jawabi ga manema labarai, Ƙauran na Bauchi ya ce ‘yan bindigar sun fara ƙarfi a sassan jihar, wanda hakan ya sa suka fara mamaye wuraren da babu shugabanci a yankin Daji Dam da ke Alƙaleri.
A cewarsa, an sha fafatawa tsakanin ‘yan binda jami’an hukumomin tsaro, amma duk da haka al’amarin na ƙoƙarin kere ƙarfin jami’an.
Ya ƙara da cewa, mutane da dama da ke rayuwa a yankin sun fara tsira zuwa jihohi da ƙananan hukumomi mafi kusa da su domin neman mafaka ga rayukansu.
Musamman gwamnan ya bayyana damuwa akan yadda suke ƙoƙarin harin yankuna masu tattalin arziƙi, yana mai bada misali da mai da gas da kuma wuraren da ake haƙar ma’adinai.
Kazalika, ya yi gargaɗin cewa rashin zaman lafiya a yankunan ka iya janyo koma-baya ga harkokin zuba jari da ci-gaban tattalin arziƙi a jihar da ta ɗauki tsawon shekaru tana amfanuwa da zaman lafiya da lumana.
