IPAC ta zaɓi sababbin shugabanni a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta yaba da tsarin zaɓen da ya samar da ɗan jam’iyyar YPP, Muka’il Abubakar, a matsayin Shugaban ƙungiyar Jam’iyyun Siyasa ta Jihar Kaduna, wato Inter-Party Adɓisory Council (IPAC).

A zaɓen da aka gudanar a ranar Alhamis, Muka’il Abubakar ya samu ƙuri’u 11 cikin 19, inda ya kayar da abokan takararsa da tazara mai yawa, domin komawa kujerar shugabancin IPAC na reshen jihar Kaduna.

Haka kuma, Musa Muhammed na jam’iyyar AAC ya zama Sakataren ƙungiyar na Kaduna bayan nasarar da ya samu a nasa ɓangaren.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala zaɓen, Shugaban Sashen Ayyukan Zabe na INEC, Mohammed Ismail, ya bayyana cewa tsarin zaɓen ya kasance cike da gaskiya, tsafta da kuma nuna kamun kai ta siyasa.

Ya ce abin da ya gani ya wuce zato, domin ba a samu hayaniya ko sabani mai tsanani ba kamar yadda ake gani a wasu zaɓuɓɓuka.

A cewarsa, “Tsarin ya kasance cikin natsuwa da bin ƙa’ida. A mafi yawan lokuta, zaɓuɓɓuka ba sa wucewa ba tare da ƙorafi ko jayayya ba, amma a nan komai ya gudana cikin kwanciyar hankali. Wannan abin a yaba ne.”

Ya kuma jinjinawa kwamitin zaɓen na IPAC bisa kyakkyawan aikin da suka yi wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

INEC ta buƙaci sabbin shugabannin IPAC a Kaduna da su yi aiki bisa dokoki da ƙa’idojin ƙungiyar, tare da tabbatar da haɗin kai tsakanin jam’iyyun siyasa domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a jihar.

A nasa ɓangaren, sabon shugaban IPAC, Muka’il Abubakar, ya yi alƙawarin jagoranci mai ma’ana da gaskiya. Ya tabbatar wa mambobin ƙungiyar cewa ba zai ci amanar amincewar da suka ba shi ba, yana mai cewa wannan nasara ta kowa ce, ba tasa kaɗai ba.

Shugaban Kwamitin Zaɓe, Bashir Bala, ya taya sabbin shugabannin murna, tare da jan hankalinsu da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin IPAC domin ci gaban siyasar jihar.

Sauran wazanda aka zaɓa sun haɗa da Solomon Ayock na ADP a matsayin Mataimakin Shugaba, Fatima Sani na PDP a matsayin Mataimakiyar Sakatare, Jemilu Muhammed na jam’iyyar Accord Party a matsayin Sakataren Kuɗi, da Hassan Saleh na APP a matsayin Ma’aji. Haka kuma, Aisha Umar Faruƙ na BOOT Party ta zama Sakatariyar Tsare-tsare, Yusuf Shuaibu na PRP ya zama Jami’in Hulɗa da Jama’a, yayin da Hassan Subaru na NNPP ya karbi muƙamin Lauya na IPAC.

A ɗaya ɓangaren kuma, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ba ta da hannu a wani zaɓe da ake zargin an gudanar a matsayin zaɓen shugabancin Ƙungiyar Jam’iyyun Siyasa (IPAC), reshen jihar Kaduna, inda ta tabbatar da cewa zaɓe guda caya kacal ta sanya ido a kansa.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishinta, INEC ta ce zaɓen da ta amince da shi shi ne wanda Kwamitin Zabe na ƙasa na IPAC ya gudanar a ɗakin taro na INEC da ke Kaduna, tare da sanya idon jami’an hukumar.

Hukumar ta jaddada cewa duk wani zaɓe da aka gudanar saɓanin wannan, to ba ta da masaniya a kansa, kuma ba shi da inganci a idonta.

A ranar Alhamis da ta gabata ne INEC ta sanya ido kan zaben IPAC na jihar Kaduna, wanda ya haifar da zaben ɗan jam’iyyar YPP, Mikailu Abubakar, a matsayin shugaban IPAC na jihar.

Sai dai wasu mutane ƙalilan sun gudanar da wani zaɓe daban, ba tare da halartar jami’an INEC ba, inda suka bayyana Ahmed Tijjani Mustapha a matsayin shugaban IPAC na Kaduna. Wannan mataki ya janyo cece-kuce tsakanin ɓangarorin siyasa a jihar.

Da yake ƙarin haske, Shugaban Sashen Ayyukan Zabe na INEC, Mohammed Ismail, ya tabbatar da cewa zaɓe guda ɗaya ne kawai hukumar ta sanya ido a kansa.

“Zaɓen da muka sanya ido a kansa shi ne kaɗai muka sani,” inji shi, yana mai jaddada cewa duk wani abu da ya sabawa haka bai shafi hukumar ba.

Tun da farko, bayan kammala zaɓen a hedikwatar INEC da ke Kaduna, Mohammed Ismail ya bayyana cewa tsarin da ya haifar da shugabancin Mikailu Abubakar da sauran ‘yan kwamitinsa ya kasance mai gaskiya da bin ƙa’ida, tare da nuna cewa an gudanar da shi cikin tsari da gaskiya.

Matakin INEC na fayyace matsayinta ya zo ne domin kauce wa ruɗani da tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda a harkokin tafiyar da al’amuran jam’iyyun siyasa a jihar.

By ukarofi