
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris, ta yi kakkausar suka game da hare-haren soji da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta bada umarnin kai wa Iran.
Ta bayyana matakin a matsayin ganganci da ka iya jefa Amurka cikin yaƙin da ba za ta so sakamakonsa ba.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Kamala Harris ta ce hare-haren wani hatsarin ƙara tsananta rikici ne, wanda ke jefa rayukan sojojin Amurka cikin haɗari tare da tada zaune tsaye a yankin da kuma rage amincewar Duniya ga jagorancin Amurka.
Harris ta bayyana matakin sojin na Amurka a matsayin caca da rayukan ’yan ƙasar, tana mai cewa hakan na barazana ga zaman lafiya na duniya da kuma martabar Amurka a idon ƙasashen waje.
A cewarta matakin na Trump ka iya ƙara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya da jefa rayukan al’ummomi cikin haɗari.
Harris ta bayyana cewa an yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙi ne ba fara sabo ba, don haka ta bukaci Majalisar Amurka ta shiga tsakani domin hana kara zurfafa rikicin.
Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da muhawara a siyasar Amurka akan matakin da gwamnatin ta dauka dangane da rikicin.
