Daga USMAN KAROFI
Wani mutum mai shekaru 43 ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zargin kashe babban ɗan’uwansa, Mustapha Amidu, a Jihar Oyo. Ana zargin mutumin ya aikata laifin ne bayan ya ce marigayin ya “harbe shi” a mafarki. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ya fitar a birnin Ibadan.
Olayinka ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Ago-Amodu ta hannun Badmus Yunisa, mazaunin unguwar Alegunlode a yankin Sepeteri. A cewarsa, wanda ake zargin ya je inda marigayin yake zaune, ya ɗauki wani babban dutse sannan ya buga masa a kai kafin ya tsere daga wurin.
An garzaya da wanda aka kai wa harin zuwa asibitin Ileri-Oluwa da ke Sepeteri domin samun kulawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa. Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru da kuma asibitin domin fara bincike. An kama wanda ake zargin, kuma ya amsa laifin, yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Femi Haruna, ya umarci a miƙa shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin zurfafa bincike.
