Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai bai wa Gwamnan Katsina shawara kan harkokin jam’iyyu, Alhaji Shafi’u Duwan yayi wannan jinjinar ga gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa kan yadda ya gudanar da zaɓuɓɓukan sabbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Katsina tun daga matakin unguwanni har zuwa na jiha.
Duwan ya ce zaɓen an yi shi cikin natsuwa, ilmi da hangen nesa wanda hakan ya ƙara saka jihar Katsina a tarihi a matsayin gagara gasa, kuma abin misali da koyi.
“Duk waɗannan nasarorin sun samu ne a bisa kyakkyawan jagorancin mai girma Gwamnan Katsina, mai hangen nesa da adalci,”Inji Duwan.
Alhaji Shafi’u Duwan ya bayyana shugabannin da aka zaɓa tun daga matakin unguwanni zuwa jiha a matsayin mutane masu kishi da cigaban Katsina da kuma jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa yana da kyakyawan zaton za su kawo ma jam’iyyar da jihar babban ci gaba a bisa tsarin mai girma gwamnan Katsina na gina yau don goben mu.
Alhaji Shafi’u Duwan ya ƙara da cewa babbar nasarar da jihar ta samu shi ne na zaɓen shugaba na jiha, wanda babu kamar sa a duk shugabannin jihohin da aka zaɓa a faɗin ƙasar nan, watau Dr Bishir Gambo Saulawa.
“Alhaji Bishir Gambo ɗan siyasa ne da ya taso da tarbiyyya a manyan gidajen siyasa. Ya kuma san zaɓe ya san cin zaɓen, ya kuma san gwamnati da yadda take tafiya, ya kuma san manufar mai girma Gwamna na tsarin sa na gina sabuwar Katsina da kafa tarihi abin misali don ‘yan baya,”Duwan ya ce.
Ya yi kira ga ya’yan jam’iyar APC a jihar da su ba sabbin shugabannin goyon baya domin samun nasarar jam’iyar a zaɓe mai zuwa .
Alhaji Shafi’u ya tabbatar wa sabon shugaban jam’iyar APC a jihar cewa zai samu goyon bayan al’ummar Katsina saboda sun san irin cigaban da ya kawo a muƙami daban daban-daban da ya riƙe a gwamnatin Katsina.
