Masu buƙata ta musamman a Kano sun buƙaci a rika naɗa su kan muƙaman da suka shafe su

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu daga cikin shugabannin masu buƙata ta musamman (Persons With Disabilities – PWDs) a Jihar Kano sun buƙaci gwamnatin jihar da ta riƙa naɗa mutane daga cikin su a muƙaman gwamnati da suka shafi harkokin nakasa, domin tabbatar da adalci da wakilci a harkokin shugabanci.

Kiran na ƙunshe ne cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da jagorancin ƙungiyar PWDs suka aike wa gwamnatin jihar Kano, inda suka bayyana cewa mutanen da ke rayuwa da nakasa su ne suka fi fahimtar ƙalubalen da ɓangaren ke fuskanta a rayuwa.

A cikin wasikar, wacce Ali Miko Muhammad Dangwauro, wanda ke daga cikin shugabannin ƙungiyar kuma kurma, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa bai dace a riƙa naɗa mutanen da ba su da nakasa domin jagorantar harkokin da suka shafi PWDs ba.

ƙungiyar ta bayyana cewa duk da suna girmama kowa, amma wadanda ba su rayu da irin wadannan kalubale ba ba za su iya fahimtar matsalolin da PWDs ke fuskanta ba kamar yadda su kansu ke ji.

Don haka ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta tabbatar cewa duk mukaman da suka shafi harkokin nakasa, kamar su masu ba da shawara (Advisers), mataimaka na musamman (S.A. da SSA), da kuma shugabanni ko mambobin hukumar kula da harkokin nakasa, ana zaɓo su ne daga cikin mutanen da ke rayuwa da nakasa.

Haka kuma ƙungiyar ta jaddada buƙatar cewa shugabannin makarantun kurame, bebaye da sauran makarantun musamman (Special Schools) su kasance daga cikin mutanen da suka ƙware a fannin tare da fahimtar halin da daliban da ke da nakasa ke ciki.

ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu malamai a bangaren Special Education ba su da cikakkiyar ƙwarewa, musamman a fannin Sign Language da Finger Spelling ga dalibai kurame, lamarin da suka ce na rage ingancin koyarwa da kuma ci gaban ɗaliban da ke da nakasa.

A cewarsu, ya kamata ma’aikatar ilimi ta jihar ta sake duba wannan batu domin tabbatar da cewa ana daukar kwararrun malamai da suka kware a irin wadannan fannoni domin inganta ilimin yara masu bukata ta musamman.

ƙungiyar ta ƙara da cewa idan aka bai wa mutanen da ke rayuwa da nakasa damar jagoranci a ɓangaren da ya shafe su, hakan zai taimaka wajen inganta manufofi da shirye-shiryen da za su taimaka musu.

“Muna da yaƙinin cewa gwamnatin jihar Kano na da burin gina al’umma mai adalci da hadin kai. Amma ba za a kai ga wannan buri ba idan wadanda abin ya shafa ba su samu damar shiga cikin tsarin yanke shawara ba,” in ji wani bangare na wasikar.

ƙungiyar ta kuma bayyana cewa nakasa ba wai gazawa ba ce, illa dai wani yanayi ne da mutum ke rayuwa da shi, kuma akwai dimbin baiwa da kwarewa a tsakanin mutanen da ke da nakasa idan aka ba su dama.

A ƙarshe, kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dauki wannan kira da muhimmanci domin tabbatar da adalci, wakilci da daidaito ga dukkanin mutanen da ke rayuwa da nakasa a jihar.

ƙungiyar ta kuma bayyana fatan cewa gwamnatin jihar za ta duba wannan bukata tare da daukar matakan da suka dace domin karfafa matsayin mutanen da ke da bukata ta musamman a cikin al’umma.

By ukarofi