
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa wajibi ne Amurka ta taka rawa wajen zaɓen sabon jagoran ƙasar Iran bayan rasuwar jagoran addini na ƙasar, Ali Khamenei.
Trump ya kuma yi watsi da yiwuwar ɗan Khamenei, Mojtaba Khamenei, ya gaji kujerar jagorancin ƙasar, inda ya bayyana shi a matsayin wanda “ba za a amince da shi ba, kamar yadda ya shaida wa Axios a wata hira.
A cewarsa, Amurka na son ganin an samu sabon shugaba a Iran wanda zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da rage tashin hankalin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sai dai har yanzu hukumomin Iran ba su mayar da martani kan wannan furuci na Trump ba, yayin da hankalin duniya ke kan yadda za a zaɓi sabon jagoran ƙasar bayan rasuwar Ali Khamenei a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila.
Trump ya kuma kwatanta halin da Iran ke ciki a yanzu da na ƙasar Venezuela, inda Delcy Rodríguez ya zama shugaba bayan harin Amurka ya yi sanadiyyar tsigewa da kama tsohon shugaban ƙasar, Nicolás Maduro.
