Akwai yiwuwar Gwamnan Dauda na Zamfara ya koma APC saboda matsalolin PDP

Spread the love

‎Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na duba yiwuwar sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki, yayin da wa’adin da Hukumar Zaɓe ta kasa (INEC) ta sanya ke ƙaratowa.

Rahotanni sun nuna cewa, wasu manyan shugabannin APC a Abuja sun yi ƙoƙarin jawo hankalin gwamnan zuwa jam’iyyar, inda ake zargin sun yi masa tayin tikitin takarar gwamna kai tsaye a zaɓen shekarar 2027 idan ya koma APC.
‎
‎A cikin yarjejeniyar da ake zargin an tattauna, za a bai wa gwamnan kashi 40 cikin 100 na muƙaman siyasa da na zaɓe a jihar, yayin da sauran kashi 60 cikin 100 za su kasance ga sauran ’yan APC a Zamfara.

Sai dai wata majiya daga cikin APC ta ce ba kowa ne a cikin jam’iyyar ke farin ciki da wannan yiwuwar sauya sheƙa ba, domin hakan na iya sa wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar su rasa muƙamansu.
‎
‎Saidai gwamnan, yayin da yake magana da masu ruwa da tsaki na PDP a Gidan Gwamnatin Gusau, ya bayyana cewa makomar siyasarsa za ta dogara ne da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke kan rikicin cikin gida na PDP.

Ya ce, idan kotu ta tabbatar da sahihancin shugabancin jam’iyyar da kuma babban taron da aka yi a Ibadan a shekarar 2025, zai ci gaba da kasancewa a PDP, amma idan rikicin ya ci gaba, hakan na iya sa a sake nazarin matakin da za a ɗauka.

By Babaji