Rufe matatun mai a duniya ya sa muka zama abar dogaron Nijeriya, inji Matatar Ɗangote

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Matatar man fetur ta Dangote ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wadatar makamashi a ƙasar, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tangarɗa a kasuwar mai ta duniya. Kamfanin ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ya janyo rufe wasu matatun mai tare da rage yawan tace man fetur a sassa daban-daban na duniya, lamarin da ya haddasa ƙarancin man fetur a kasuwannin duniya.

Kamfanin ya ƙara da cewa wasu ƙasashe sun fara ɗaukar matakai domin kare kasuwanninsu, inda ƙasar Sin ta dakatar da fitar da man fetur da dizal zuwa ƙasashen waje. Hakan ya sa farashin ɗanyen mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi, inda farashin ya ƙaru da kusan kashi 26 cikin ɗari zuwa sama da dala 84 kan ganga. Matatar Ɗangote ta bayyana cewa saboda wannan yanayi ta yi ƙarin naira 100 kan kowace lita ta man fetur daga farashin da ake sayarwa a ma’ajiyarta.

Sai dai kamfanin ya jaddada cewa ya ɗauki wani ɓangare na ƙarin kuɗin da kansa domin rage nauyi ga ‘yan Najeriya, duk da cewa yana sayen ɗanyen mai ne a farashin kasuwar duniya. Kamfanin ya kuma ce matatar mai ta cikin gida na taimakawa wajen rage matsin lamba daga kasuwar waje, tare da tabbatar da wadatar mai a Najeriya, inda kuma yake shirin fara amfani da manyan motoci masu amfani da CNG domin inganta rabon man fetur a faɗin ƙasar.

By ukarofi