Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Adamu Atiku-Abubakar ya ajiye muƙaminsa a matsayin kwamishinan ayyuka da bunƙasa makamashi na jihar Adamawa.
Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Abdulaziz Jauro, ne ya sanar da hakan.
Ana dai sa ran ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai koma jam’iyyar ADC.
Tsohon kwamishinan ya gode wa gwamna Ahmadu Fintiri “kan ba shi dama da ganin cancantarsa na rike muƙamin.”
Ya kuma bayyana cewa wannan dama karramawa ce a gare shi inda ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa shirin gwamnatin baya na kawo ci gaba a jihar.
“Tsohon kwamishinan ya miƙa godiyar ga mahaifinsa kan yi masa jagoranci da damar hidimta wa al’ummar jihar Adamawa”
“Ya kuma yaba wa sakataren dindin na na ma’aikatar ayyuka da makamashi da daraktoci da injiniyoyi da ɗaukacin ma’aikata kan irin nuna ƙwarewa da juriya da sadaukarwa wajen bunƙasa jihar,” ya bayyana.
Atiku-Abubakar ya ce, “ajiye muƙaminsa ba yana nuna cewa ya daina hidimta wa al’umma, wannan ma shi ne masomi na ganin kawo ci gaba.”
“Ya nuna aniyarsa ta ci gaba da ba da gudunmowa wajen ci gaba da haɗin kai da haɓaka jihar Adamawa,” a cewar sanarwar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da gwamna Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC tare da sauran muƙarrabansa da manyan jami’an gwamnati.
