Kofin Duniya na 2026: FIFA ta sanar da wa’adin ƙarshe na mika jerin ‘yan wasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA, ta ayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin lokacin da za ta rufe amsar jerin sunayen ‘yan wasan ƙasashen da za su fafata a gasar Kofin Duniya na 2026.

A cewar umarnin, kowace ƙasa wajibci ne ta miƙa tawagar sunayen ‘yan wasa guda 25 domin fafatawa a gasar, wanda haka aka yi a lokacin gasar ta 2022.

Wannan mataki ya bai wa tawagogin ƙasashen damar ɗaukar adadin ‘yan wasa masu yawa domin magance dukkan wasu matsaloli da ka iya shafar su kamar na jin rauni, daktarwa da kuma rashin wadataccen hutu ga ‘yan wasa yayin da ake tsaka da gudanar da wasan.

Ana tsammanin masu horarwa su kammala fitar da jerin ‘yan wasan da suke so su wakilci ƙasashen da suke jagoranta gabanin wa’adin da FIFA ta bayar ya cika.

‘Yan wasan da aka yi wa rajista ne kaɗai za su cancanci shiga gasar da zarar an miƙa jaddawalin jerinsu ga hukumar.

A wannan karo ana sa ran gasar ta 2026 za ta kafa sabon tarihi yayin aka zaɓi ƙasashe huɗu su jagorance ta waɗanda suka haɗa da Amurka, Kanada da kuma Mexico. Sannan ƙasashe 48 ne za su fafata a ciki.

By Babaji