An samu ƙarin matsi ga ‘yan Nijeriya yayin da Ɗangote ya sake ƙara farashin fetur sa’o’i bayan ragewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Farashin fetur ya sake hawa zuwa N1,175 a matatar Dangote sa’o’i bayan sanar da ragewa.

Matatar ta sake ɗaga farashin fetur zuwa N1,175 akan kowace lita.

A baya dai matatar ta rage farashin fetur da N100, wanda farashin ya sauka zuwa N1,075 akan lita a ranar 10 ga Maris, 2026, wato daga N1,175.

Bayan sabon karin farashin, masu sayar da mai a manyan rumbunan ajiya (depots) sun dakatar da sayar da fetur na ɗan lokaci domin tantance sabon tsarin farashin.

Wannan al’amari ya sake jefa ‘yan Nijeriya cikin matsi musamman bisa la’akari da halin da ake ciki na matsin tattalin arziƙi da al’umma ke fuskanta na tsawon lokaci.

By Babaji