
Babbar Kotun Tarayya ta ba Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC izinin shiga da binciken bayanai daga wasu na’urorin lantarki da aka kwato daga gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis bayan ta amince da bukatar da ICPC ta gabatar ta hannun lauyanta, Dr. Osuobeni Akponimisingha.
ICPC ta bayyana cewa tana bukatar duba na’urorin ne domin gudanar da binciken fasaha (forensic examination) da kuma fitar da bayanai domin ci gaba da binciken da take yi kan tsohon gwamnan.
Na’urorin da ake son bincika sun hada da: wayoyin Samsung, Nokia, Blackberry da ZTE, kwamfutar Apple MacBook Pro, wani tablet, hard drives daban-daban, flash drives guda 10.
Kotun ta kuma amince a binciki bayanai kamar takardun gwamnati, tattaunawar WhatsApp, sakonnin waya, hotuna da bayanan kira domin tantance su a binciken.
Binciken ICPC kan El-Rufai na ci gaba, yayin da kotu ta ba da damar zurfafa bincike kan bayanan na’urorin da aka kwato gidan sa dake Abuja.
