Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya taya wasu ‘yan jihar biyu, Bello Shehu da Dankombo Morris Fallings, murna kan ɗaga su zuwa muƙamin mataimakan babban sufeton ‘yan sanda ta Najeriya.
A cikin saƙon taya murna da aka fitar ranar Jumma’a ta bakin darakta janar na harkokin yaɗa labarai na fadar gwamnati, Isma’ila Uba Misilli, gwamnan ya bayyana cewa wannan ɗaga muƙamin ya nuna yabo ne ga shekaru da suka shafe suna aiki tuƙuru, ƙwarewa da hidimar da suka bayar a cikin rundunar ‘yan sanda.
Gwamnan ya ce wannan ɗaga muƙamin na nuna irin jajircewa, ladabi da gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa manyan jami’an biyu sun gina kyawawan ayyuka a cikin rundunar ‘yan sanda, wanda aka yi fice da nagarta, gaskiya da jajircewa wajen jagoranci da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma tunatar da irin ayyukan da suka yi yayin da suke mukamin Sufeton ‘yan sanda a jihohi daban-daban, inda ya ce Bello Shehu ya nuna bajinta a fannin shugabanci da gudanar da aiki yayin da yake sufeton ‘yan sanda a Jihar Katsina.
Haka kuma, ya yabawa Dankombo Morris Fallings bisa ƙwarewa da ingantaccen shugabanci yayin da yake Sufeton ‘Yan Sanda a Jihar Adamawa.
Gwamnan ya ce gwamnati da mutanen Jihar Gombe suna alfahari da irin nasarorin da jami’an suka samu, inda ya bayyana cewa ɗaga mukamin su wani lokaci ne na yabo da alfahari ga jihar.
“Ɗaga ku zuwa muƙamin Mataimakan Babban Sufeton ‘Yan Sanda yana nuna shekaru da kuka shafe kuna aiki tuƙuru, ladabi da gudunmawar da kuka bayar wajen tsaro da kiyaye doka a ƙasa,” in ji gwamnan.
Gwamna ya bayyana cewa Bello Shehu dan Gombe LGA ne, yayin da Dankombo Morris Fallings dan Kaltungo LGA ne a jihar.
Ya kuma yi kira ga manyan jami’an da aka ɗaga su da su ɗauki wannan mukami a matsayin kiran ci gaba da hidima ga ƙasa, tare da ci gaba da bin ƙa’idojin aiki, gaskiya da kishin ƙasa a lokacin gudanar da aikinsu.
