ICPC ta gano kadarori na biliyoyin naira da ake zargin suna da alaƙa da El-Rufai a Misra 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Masu bincike na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, sun gano wasu kadarori masu darajar biliyoyin naira a ƙasar Egypt da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cewar wasu jami’ai da ke da masaniya kan binciken kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Majiyoyi a cikin hukumar sun ce an sayi kadarorin ne tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023.

Wasu majiyoyi daga cikin jami’an hukumar, waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin magana a bainar jama’a, sun bayyana cewa kadarorin suna cikin manyan unguwanni na New Cairo, wani sabon yanki da ke ci gaba da bunƙasa wa a wajen birnin Cairo, wanda ya shahara da gidaje masu tsada da kuma gidajen da ke cikin keɓaɓɓun unguwanni.

A cewar masu binciken, bayanan da hukumar ta samu sun nuna cewa wasu manyan gidaje (villas) da gidajen haya a yankin na iya kasancewa suna da alaƙa da tsohon gwamnan. An ce kadarorin suna cikin wasu daga cikin manyan wuraren zama na New Cairo, ciki har da Arabella Estate, Banafsek Estate, Oriana Estate da kuma Cairo Festival City.

Rahotanni sun nuna cewa farashin manyan gidaje a Cairo Festival City da Arabella na kaiwa tsakanin fam miliyan 50 zuwa miliyan 200 na Egypt, wanda ya kai kusan naira biliyan 5.3, yayin da farashin gidajen haya ke kusan fam miliyan 26 na Egypt, wato kusan naira miliyan 700.

Wani jami’in bincike ya ce daga cikin kadarorin da ake dubawa akwai wani gida mai lamba 113 a Arabella Estate da ke yankin Fifth Settlement na New Cairo. Haka kuma ana zargin wani gida mai lamba 18 a Banafsek Estate da ke First Settlement yana da alaƙa da El-Rufai.

Masu binciken sun kuma ambaci wani gida a Oriana II Estate kusa da American University in Cairo, wanda aka ce yana da lamba 11.

Baya ga manyan gidajen, hukumar ta kuma gano wasu gidajen haya a Cairo Festival City, inda ake binciken gidaje huɗu masu lambobi 514, 515, 516 da 517.

Haka kuma ana duba wasu gidajen haya biyu a Oriana Estate masu lambobi 4000 da 4100 a matsayin wani ɓangare na binciken da ake yi.

Wani jami’i da ke cikin binciken ya ce suna nazarin rahotannin sirri tare da bin diddigin tsarin mallakar kadarorin.

Ya ƙara da cewa ana kuma duba rajistar kadarori da hanyoyin kuɗin da aka bi wajen sayen su, tare da bin hanyoyin diflomasiyya da na shari’a saboda kadarorin suna wajen Nijeriya.

Sai dai jami’an hukumar sun ƙi bayyana ƙarin bayani saboda muhimmancin binciken.

ƙoƙarin jin ta bakin iyalan El-Rufai bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, yayin da ICPC ita ma ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da zargin ko matsayin binciken ba.

By ukarofi