Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour Party a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, yana cewa ƙasar ta shiga wani yanayi mai matuƙar muni sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda a sassa daban-daban.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ a safiyar Litinin, Obi ya ce hare-haren sun yi ƙamari matuƙa, inda al’ummomi da dama ke fuskantar farmaki akai-akai, yayin da shugabanni ke ci gaba da yin shiru kan lamarin.
Ya bayar da misali da wani hari da aka kai a garin Ngoshe da ke jihar Borno, inda ya ce ‘yan ta’adda sun yi nasara kan sojoji, suka kashe wasu daga cikinsu tare da fararen hula, sannan suka yi garkuwa da mata da yara sama da 100.
Obi ya kuma jaddada cewa sadaukarwar da sojojin Nijeriya ke yi wajen kare ƙasa ba a cika yabawa yadda ya kamata ba. Ya bayyana fatan cewa wata rana shugabanni za su fara girmama sojojin da suka rasu yayin aikin kare ƙasa ta hanyar yi musu jana’iza mai cike da karramawa.
Har ila yau, ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke taɓarɓarewa a jihohi da dama, ciki har da Nasarawa, Kogi da Benue, inda ya ce ‘yan ta’adda ke shiga gonaki da dazuka suna hana mutane gudanar da harkokin noma, tare da tilasta wa wasu al’ummomi barin muhallansu.
A cewarsa, a yankin Kadarko an riga an yi rajistar mutane 14,318 a matsayin ‘yan gudun hijira sakamakon hare-haren.
Obi ya kuma ambaci wasu hare-hare da suka faru a wasu jihohi, ciki har da Oyo inda aka yi garkuwa da matafiya a hanyar Kishi zuwa Igbeti, da kuma Ondo inda aka harbe wasu fararen hula tare da sace wasu.
Haka kuma ya ce a jihar Kebbi, ‘yan ta’adda na ci gaba da kai hare-hare inda suke kashe jami’an tsaro da fararen hula.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta kai har babban birnin tarayya Abuja, inda aka yi garkuwa da mutane a yankin Kubwa.
