ADC za ta bada mamaki a zaɓen 2027, inji jigo a jam’iyyar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani jigo a jam’iyyar ADC, Cif Ogochukwu Agabus Umunnakwe Onyema, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na da ƙwarin gwiwar kawo babban sauyi a zaɓen shekarar 2027, inda ya ce ADC za ta ba da mamaki a siyasar Nijeriya.

Onyema ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a birnin Enugu, inda ya ce shugabancin jam’iyyar ADC a halin yanzu yana da tsari mai kyau tare da ƙudurin kwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki ta APC a babban zaɓen da ke tafe.

Ya ce, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a siyasar ƙasar, jam’iyyarsa na da yakinin samun nasara idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yiwuwar maguɗin zaɓe da zai iya karkatar da sakamakon zaɓe, amma duk da haka ya jaddada cewa ADC za ta iya ba da mamaki idan aka yi komai cikin gaskiya.

A cewarsa, abubuwa da dama ne ke tasiri a siyasar Nijeriya, musamman yadda rashin ladabi da gaskiya ke ƙara bayyana a harkokin mulki.

Ya ce idan aka samu mutunta ƙa’idoji da gaskiya a harkokin siyasa, al’amura za su gyaru sosai, amma saboda yadda ake samun taɓarɓarewar ɗabi’u, sau da yawa abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata.

Onyema ya kuma yi kira ga ɓangaren shari’a da sauran masu ruwa da tsaki a tsarin mulkin ƙasar da su tsaya tsayin daka wajen yin abin da doka ta tanada domin tabbatar da adalci.

Ya ƙara da cewa, jama’ar Nijeriya na da sha’awar ganin canji mai kyau a harkokin shugabanci, amma hakan na buƙatar kowa ya sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata.

“Idan duk masu ruwa da tsaki a tsarin mulki za su yi abin da ya dace, Nijeriya za ta ga babban sauyi mai kyau. Jama’a na shirye su rungumi sauyi, amma akwai buƙatar a dawo da adalci da gaskiya cikin tafiyar da gwamnati,” inji shi.

Daga ƙarshe, Onyema ya bayyana cewa idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da bin doka, jam’iyyar ADC za ta iya girgiza siyasar Nijeriya a zaɓen 2027.

By ukarofi