Farashin abinci ya ragu da kashi 50 a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Noma da Tsaron Abinci na Tarayya, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa sabon mayar da hankali da gwamnatin ƙasa ta yi kan harkar noma ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda farashin kayayyakin abinci a faɗin Nijeriya ya ragu da kusan kashi 50 cikin ɗari.

Ministan ya bayyana haka ne a wani zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ’yan ƙasa da aka gudanar a birnin Abuja ranar Juma’a.

Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta sanya batun tsaron abinci a sahun gaba na manufofinta na ƙasa, saboda muhimmancinsa wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki da kuma kare martabar ƙasa.

A cewarsa, dabarun da gwamnati ke bi sun mayar da hankali ne kan ƙarfafa samar da abinci a cikin gida tare da rage dogaro da shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya suna samun abinci mai arha kuma mai gina jiki.

Kyari ya jaddada cewa tsaron abinci na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiyar ƙasa, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da ƙarfafa manoma domin su samar da abinci cikin yawa, ta yadda za a rage matsin tattalin arziki da kuma sauƙaƙa rayuwar jama’a.

Ministan ya ƙara da cewa, matakan da gwamnati ta ɗauka sun fara bayyana a fili a kasuwannin abinci a sassan ƙasar, inda farashin kayayyakin abinci masu muhimmanci ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya da farashi ya tashi sama da yadda mutane da dama za su iya biya.

Ya ce, Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin ci gaba da ɗorewar wannan sauƙi ta hanyar magance matsalolin tsadar samar da kayayyaki da kuma kayan aikin noma.

A cewarsa, gwamnati ta kuma ƙara ƙaimi wajen bunƙasa manyan sassan darajar noma domin mayar da Nijeriya wata muhimmiyar ƙasa a kasuwar noma ta duniya. Daga cikin amfanin gona da aka ba fifiko akwai shinkafa, masara, alkama, gero, dawa, doya, koko, wake, rogo, waken suya, auduga, albasa, tumatir da kuma dabino mai.

Kyari ya bayyana cewa shirye-shiryen da gwamnati ta aiwatar tsakanin shekarun 2024 zuwa 2025 sun haɗa da rarraba ingantattun iri, magungunan gona, kayan kariya ga manoma, da kuma kayan yaƙi da kwari da cututtukan amfanin gona. Haka kuma an gudanar da shirye-shiryen horaswa domin ƙara wa manoma ƙwarewa.

A cewarsa, waɗannan matakai sun taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, rage asarar da ake yi bayan girbi, da kuma inganta ingancin kayayyakin noma.

Ministan ya ƙara da cewa, wannan shiri ya taimaka wa manoma ƙanana da dama su fita daga tsarin noma na dogaro da kai kawai zuwa harkar kasuwancin noma, lamarin da ke taimakawa wajen samar da abinci ga ƙasa, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Yayin da yake gabatar da bayanin nasarorin da aka samu cikin shekaru biyu da suka gabata, Kyari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta rarraba buhunan takin zamani sama da miliyan 1.9 ga kusan manoma miliyan ɗaya a faɗin ƙasar.

Ya kuma ƙara da cewa an samar da kimanin lita dubu 12 na takin gargajiya domin ƙarfafa hanyoyin kula da ƙasa ta yadda za ta ci gaba da bada amfanin gona mai kyau.

Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ƙarfafa tsarin doka da sa ido a masana’antar takin zamani domin tabbatar da inganci da kuma hana yaɗuwar taki na jabu a kasuwa.

Kyari ya ƙara da cewa ma’aikatar noma ta faɗaɗa haɗin gwiwa da wasu ƙasashe kamar Rasha, Turkiyya, Indiya da Kanada, domin tallafa wa samar da taki, musayar fasaha da kuma ƙirƙire-ƙirƙire a fannin noma.

A ɓangaren sa ido kan harkar takin zamani kuwa, ministan ya ce an horas da jami’an dubawa 109 domin su riƙa sa ido kan ingancin kayayyakin da ake samarwa, yayin da sama da masu ruwa da tsaki 329 aka horar kan bin ƙa’idojin masana’antar.

Ya kuma jaddada cewa hukumomi sun ƙara tsaurara matakan yaki da masu sayar da takin jabu, inda ake kamo masu laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu.

A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa wannan dandalin tattaunawa da ’yan ƙasa ya yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ke ƙarfafa sanar da jama’a game da shirye-shiryen gwamnati tare da sauraron ra’ayoyinsu.

Malagi ya ce gwamnati na kuma aiwatar da shirye-shirye domin tallafa wa rukunin jama’a masu rauni da kuma buɗe ƙarin damar ci gaba ga matasan Nijeriya.

Ya bayyana cewa Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta Tarayya ta faɗaɗa noman rani, ta inganta tsarin rarraba taki, ta ƙarfafa amfani da injinan noma, tare da zurfafa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da ƙungiyoyin raya ƙasa.

A cewarsa, waɗannan matakai na taimakawa wajen inganta hanyoyin samar da abinci da kuma tallafa wa manoma a sassan Nijeriya.

Ministan ya ƙara da cewa burin gwamnati ba wai kawai samar da wadataccen abinci ga ƙasar ba ne, har ma da mayar da Nijeriya babbar ƙasa mai fitar da kayayyakin noma zuwa kasuwannin duniya.

Ya kuma jaddada cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun fahimci manufofi da tsare-tsaren gwamnati da kuma inda take nufi.

By ukarofi