Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fitaccen ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, ya sake riƙe matsayinsa na mutum mafi arziki a nahiyar Afirka, bayan da mujallar tattalin arziki ta duniya ta fitar da jerin attajiran Afirka na shekarar 2026.
Rahoton ya nuna cewa dukiyar Dangote ta kai kimanin dala biliyan 28.5, abin da ya sa ya ci gaba da zama na ɗaya a jerin.
Sabon rahoton da mujallar Forbes ta fitar ya kuma nuna cewa attajiran Afirka sun ƙara tara sama da dala biliyan 20 cikin dukiyarsu a cikin shekara guda da ta gabata, sakamakon bunƙasar kasuwanni da kuma daidaituwar kuɗaɗen wasu ƙasashen nahiyar.
A cikin jerin attajiran, ’yan Nijeriya huɗu ne suka samu gurbi, wato Aliko Dangote, Mike Adenuga, Abdulsamad Rabiu da Femi Otedola, lamarin da ke nuna irin tasirin da ’yan kasuwar Nijeriya ke da shi a fannin tattalin arzikin Afirka.
Rahoton ya bayyana cewa dukiyar Dangote ta ƙaru da kusan dala biliyan 4.6 a cikin shekarar nan. Hakan ya biyo bayan hauhawar darajar hannun jarin kamfaninsa na Dangote Cement, wanda ya ƙaru da kusan kashi 69 cikin ɗari tun daga watan Maris na shekarar da ta gabata, bayan kamfanin ya ninka ribarsa a shekarar 2025 zuwa sama da naira tiriliyan ɗaya.
Haka kuma Dangote ya sanar da wata yarjejeniya ta kusan dala miliyan 400 da wani kamfanin ƙera injuna na ƙasar Sin domin hanzarta shirinsa na ninka ƙarfin tace mai na matatar man fetur ɗinsa nan da shekarar 2029.
A ɓangaren ƙarin dukiya kuwa, Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, shi ne ya fi samun riba a jerin. Dukiyarsa ta ƙaru da kusan kashi 120 cikin ɗari, inda ta tashi daga kusan dala biliyan 5 zuwa dala biliyan 11.2. Wannan ya sa ya tashi daga matsayi na shida zuwa na uku a jerin attajiran Afirka.
Darajar hannun jarin BUA Cement ta ƙaru da kusan kashi 135 cikin ɗari, abin da ya zarce ci gaban kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya wadda ta samu ƙaruwa da kusan kashi 81 cikin ɗari.
A gefe guda kuma, attajirin Afirka ta Kudu Johann Rupert ya ci gaba da riƙe matsayi na biyu a jerin da dukiyar kusan dala biliyan 16.1.
Rahoton ya kuma nuna cewa attajirin Masar Nassef Sawiris shi ne kaɗai wanda dukiyarsa ba ta ƙaru ba ko ta ragu ba a cikin shekarar nan, inda aka kiyasta dukiyarsa a kan dala biliyan 9.6. Sawiris yana da hannun jari a kulob din ƙwallon ƙafa na Ingila Aston ɓilla da kuma kamfanin kayan wasanni na duniya Adidas.
Sai dai kuma wasu attajirai guda huɗu sun fuskanci raguwar dukiyarsu a cikin shekarar. Daga cikinsu akwai attajirin Moroko Anas Sefrioui, wanda ya rasa kusan dala miliyan 300 bayan darajar hannun jarin kamfaninsa na gidaje ta ragu da sama da kashi 30 cikin ɗari.
Haka zalika, attajirin Nijeriya Femi Otedola ya rasa kusan dala miliyan 200, amma duk da haka ya sake komawa cikin jerin bayan ya sayar da mafi yawan hannun jarinsa a kamfanin Geregu Power. A halin yanzu ana kiyasta dukiyarsa a kan dala biliyan 1.3.
Mujallar Forbes ta bayyana cewa jimillar dukiyar attajiran Afirka guda 23 da ke cikin jerin ta kai dala biliyan 126.7, wanda ya nuna karin kashi 21 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2025.
Rahoton ya kuma nuna cewa mutane 14 daga cikin attajiran (kashi 61) sun gina dukiyarsu da kansu, ba tare da gado ba, yayin da babu mace ko ɗaya a cikin jerin na wannan shekara.
Dangane da rarrabuwar ƙasashe kuwa, Afirka ta Kudu ce ke da mafi yawan attajirai da guda 7, sai Masar da guda 5, sannan Nijeriya da guda 4, yayin da Moroko ke da guda 3.
A jerin shekarar 2026, mafi yawan attajiran nahiyar sun haura shekaru 60, sai dai attajirin Tanzaniya Mohammed Dewji ne kaɗai wanda bai kai wannan shekarun ba.
