Gwamnatin Tarayya ta fallasa shirin tozarta Tinubu yayin ziyarar Birtaniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wani shiri da wasu kamfanonin haƙar ma’adinai na ƙasashen waje ke yi domin ɓata wa Shugaba Bola Tinubu suna a yayin ziyararsa a Birtaniya.

A cewar Ma’aikatar Ci-gaban Ma’adinai da Ƙarafuna ta Ƙasa, wani kamfani mai suna Jupiter Ltd na shirin kaddamar da manufa ta yaɗa jita-jita da ɗaukar nauyin zanga-zanga domin kunyata shugaban ƙasar a lokacin ziyarar.

Mataimakin Ministan Ma’adanai kan harkokin yaɗa labarai, Segun Tomori, ya ce kamfanin na shirin ɗaukar nauyin kamfen a kafafen yaɗa labarai domin sukar gwamnatin tarayya kan matakan da take ɗauka wajen tsaurara dokokin hakar ma’adanai a ƙasar.

Ana sa ran Tinubu zai kai ziyarar kwanaki biyu zuwa Birtaniya tare da matarsa, Oluremi Tinubu. Wannan ita ce ziyarar ƙasa ta farko da Nijeriya za ta kai a Windsor Castle cikin shekaru 37, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

By Babaji