
Jami’an Rundunar Sojoji sun yi nasarar kama wani matashi da ake zargi da alaka da ‘yan bindiga mai suna Sule Yalo, wanda aka ce yana amfani da shafin TikTok da sunan @suleyellow6, bayan zargin cewa yana karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka sace tare da tallata ayyukan ‘yan bindiga a kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Sule Yellow ne bayan jami’an tsaro sun fara zargin sa sakamakon yadda yake bayyana a shafukan sada zumunta da kuma alakar da ake zargin yana da ita da wasu masu aikata laifuka.
An kuma ce a ranar 4 ga watan Maris, matashin ya bayyana a wani bidiyo na TikTok tare da wani mutum da ake kira Auta da wasu mutane, lamarin da ya ƙara janyo hankalin jami’an tsaro kafin daga bisani su kai samame su kama shi.
Bayan kama shi, rahotanni sun ce an rufe ko kuma an dakatar da shafin TikTok ɗin nasa.
Wannan lamari ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin dakile ayyukan ‘yan bindiga da kuma duk wanda ake zargi da taimaka musu, ko tallata su, ko kuma amfana da kudin fansa ta hanyar amfani da dandalan yanar gizo.
