Isra’ila ta yi iƙirarin halaka Shugaban rundunar tsaron Iran a yaƙin Gabas ta tsakiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Tsaron Isra’ila, Isreal Katz, ya bayyana cewa Ali Larijani, Shugaban dakarun tsaron Iran, an hallaka shi a wani farmaki da aka kai da daddare.

A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron Isra’ila, Katz ya ƙara da cewa Gholamreza Soleimani, shugaban rundunar Basij, shima an kashe shi a wannan aiki guda.

Rundunar Basij, wadda ɗaya ce daga cikin muhimman sassan Islamic Revolutionary Guard Corps IRGC, tana da babban rawa wajen tsaron cikin gida na Iran.

Hakan na zuwa ne ƙasa da makonni uku da aka fara gwabza yaƙi tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila a ɗaya gefen.

By Babaji