Tinubu ya umarci jagororin tsaro su koma Maiduguri bayan munanan hare-haren ƙunar baƙin-wake

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci jagororin rundunonin tsaro da su gaggauta komawa Maiduguri bayan wasu munanan hare-haren ƙunar baƙin-wake da suka auku a birnin na Jihar Borno a jiya Litinin.

Tinubu ya ɗauki matakin ne da nufin ƙarfafa ayyukan tsaro a shiyyar da ke fama matsalar taɓarɓarewar harkar.

A wata takarda ga manema labarai, Shugaban ƙasar ya bayyana kaɗuwarsa game da rasa rayukan da aka yi da kuma jikkata da wasu suka samu a sanadiyyar faruwar tashin ababen fashewar, yana mai jajenta wa iyalai da abokan arziƙi game da rashin da aka yi musu.

Shugaban ya bayyana hare-haren a matsayin yunƙurin dangogin ‘yan ta’adda ciki har da Boko Haram na jefa tsoro acikin al’umma sakamakon matsin lamba a gare su daga dakarun tsaro.

Ya bayyana cewa, farmakin alamu ne na daƙile ayyukan tayar da ƙayar baya, yana mai cewa ƙoƙarin sojoji a yanzu ya lallasa ƙarfin ‘yan ta’adda da ke ayyukansu a shiyyar.

Tinubu ya kuma, ya umarci hukumomin agajin gaggawa da su tabbatar da sun ba wa duk waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace.

A ƙarshe, Shugaban ya jaddada cewa babu wani lungu a Nijeriya da zai zama wurin ɓuya ga ’yan ta’adda, inda ya ce: “Ba za mu taɓa miƙa wuya ga tsoro ba. Za mu nemo su, mu fuskance su, kuma mu murƙushe su baki ɗaya.”

By Babaji