Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC), ta sanar da ƙaddamar da wani gagarumin shirin sintiri na musamman domin bukukuwan ƙaramar Sallah na shekarar 2026, a wani mataki na ƙara tsaurara matakan tsaro da rage haɗurra a manyan hanyoyin ƙasar.
Babban Kwamandan Hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayar da wannan umarni, inda ya buƙaci a tura jami’ai da kayan aiki zuwa sassan ƙasar baki ɗaya daga ranar 17 zuwa 22 ga watan Maris domin gudanar da wannan aiki na musamman.
Ya bayyana cewa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke yi na rage yawan haɗurran mota, mace-mace da raunuka, musamman a lokacin Sallah da ake yawan zirga-zirgar ababen hawa a faɗin ƙasa.
A cewarsa, jami’an FRSC za su riƙa gudanar da sintiri na sa’o’i 24 a manyan hanyoyi, tare da taimakon motocin ɗaukar marasa lafiya, motocin ja, babura da sauran kayan aiki na gaggawa domin ceto rayuka cikin sauri idan buƙatar hakan ta taso.
Haka kuma, ya ce za a mayar da hankali wajen kawar da duk wani cikas a hanyoyi cikin gaggawa, tare da sa ido kai tsaye kan zirga-zirgar ababen hawa domin rage cinkoso da jinkiri ga matafiya.
Kwamandan ya ƙara da cewa hukumar za ta tsaurara matakan hukunta masu karya dokokin hanya, ciki har da gudun wuce kima, tuƙin ganganci, lodin da ya wuce kima, amfani da waya yayin tuƙi, rashin bin layin hanya da kuma amfani da ababen hawa marasa inganci.
Ya jaddada cewa wannan aiki zai samu goyon bayan wayar da kan jama’a domin ƙarfafa bin dokokin hanya da kare rayuka.
Bugu da ƙari, an umarci shugabannin sassan hukumar da su tabbatar da cikakken amfani da kayan aiki na zamani kamar na’urar auna gudu, na’urar gano maye, motocin ɗaukar marasa lafiya masu inganci da na’urorin sadarwa.
Hukumar za ta kuma haɗa kai da sauran hukumomin tsaro kamar ’yan sanda, DSS, Sibil Difens, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa domin tabbatar da ingantaccen tsaro da saurin ɗaukar mataki a kan hanyoyi.
An bayyana cewa wannan shiri na musamman zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa matafiya sun isa inda suka nufa cikin aminci a lokacin bukukuwan Sallah.
