Kungiyar Izala a Kano ta tallafa wa marayu da kayan abinci da tufafi

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kungiyar Izalatul Bid’a Wa I ƙamatus Sunnah (IZALA) reshen jihar Kano,  ƙar ƙashin jagorancin Farfesa Imam Abdullahi Saleh Pakistan, ta raba tallafin kayan abinci da tufafi ga gidajen marayu, tare da jaddada muhimmancin kula da su da kuma aurar da iyayen marayu.

An  ƙaddamar da rabon tallafin ne a harabar Masallacin Tudun Murtala, a wani bangare na ayyukan jin  ƙai da  ƙungiyar ke gudanarwa a  ƙarshen watan Ramadan kowace shekara.

Da yake jawabi a madadin shugaban  ƙungiyar, mataimakin shugaban IZALA na jihar Kano, Sheikh Muhammad Ahmad Usman Bichi, ya ce shirin tallafa wa marayu ya da ɗe yana gudana, kuma ya zama abin koyi ga wasu jihohi da ma gwamnatoci da suka fara kwaikwayon irin wannan tsari.

Ya bayyana cewa Imam Abdullahi Pakistan yana yawan jaddada muhimmancin tsoron Allah da kuma tallafa wa marayu, musamman duba da irin halin da suke ciki na rashin kulawa da gata irin na yara masu iyaye.

Sheikh Bichi ya ce ya dace a rika kula da marayu kamar yadda ake kula da ‘ya’ya, ta hanyar ba su abinci, ilimi, sutura da tarbiyya iri  ɗaya, domin kada su ji bambanci a cikin al’umma.

“Ba daidai ba ne a ware marayu a wani wuri daban, domin hakan na iya hana su samun tarbiyya irin ta ‘ya’yan gida. Ya kamata su ji cewa su ma ba su da wani bambanci,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga al’umma da kada su bar nauyin tallafa wa marayu ga masu hali ka ɗai, yana mai cewa ko da  ƙaramin taimako ne yana da matu ƙar muhimmanci a wajen Allah.

A nasa jawabin, shugaban majalisar malamai na  ƙungiyar IZALA a Kano, Malam Hussain Ya’ ƙub Rano, ya bayyana cewa marayu na da bu ƙatar kulawa a kowane lokaci, ba wai a watan Ramadan ka ɗai ba.

Ya bayar da misalin wasu marayu da ake tallafawa wa ɗanda har wanka ba sa yi yadda ya kamata saboda rashin ku ɗin sayen ruwa, yana mai cewa wannan na nuna tsananin halin da wasu ke ciki.

Malam Rano ya kuma jaddada muhimmancin auren iyayen marayu, yana mai cewa rashin son auren mace mai yara na daga cikin matsalolin da ke  ƙara jefa su cikin  ƙunci.

“Wasu mata na rasa damar aure ne saboda suna da yara, alhali idan aka aure su da kyakkyawar niyya, hakan zai zama alkhairi mai girma a wajen Allah,” in ji shi.

Ya  ƙara da cewa duk wanda ya yi hidima ga marayu da kyakkyawar niyya, Allah zai saka masa da natsuwa a rayuwa tare da kula da iyalansa.

A yayin  ƙaddamar da rabon tallafin, sakataren kwamitin tattara tallafin, Malam Sani Jibrin, ya bayyana sunayen mutane da kamfanonin da suka bayar da gudummawa, wanda ya taimaka wajen samar da kayan da aka rabawa marayun.

 ƙungiyar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da taimaka wa marayu a kowane lokaci, domin hakan na daga cikin manyan ayyukan lada a Musulunci.

By ukarofi