Tinubu ya sauka a Legas bayan dawowarsa Nijeriya daga Birtaniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya, inda ya sauka a birnin Lagas a safiyar yau Juma’a, 20 ga Maris, 2026, domin halartar bukukuwan Ƙaramar Sallah.

Dawowarsa na zuwa ne bayan kammala wata ziyara ta kwanaki biyu ta aiki da ya kai Birtaniya, wadda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan hulɗoɗin difulomasiyya tsakanin ƙasashen biyu a ‘yan shekarun nan.

Shugaban ƙasar ya yi Sallah tare da al’umma, inda bayan haka ne kuma zai cigaba da wasu muhimman ayyukan gwamnati bayan hutun Sallah.

Daga cikin waɗanda suka tarbe shi a Legas akwai Maitaimakin gwamna, Femi Hamzat; Shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, Matar Gwamna, Dakta Claudiana Ibijoke Sanwo-Olu, da kuma wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC.

By Babaji