Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da na mulki da gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na ƙara ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya, tare da buɗe ƙofofi na sabbin damar kasuwanci, zuba jari da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Litinin, ya ce ministan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a birnin London, yayin wani taron manema labarai na duniya gabanin ziyarar aiki da Shugaba Tinubu zai kai Birtaniya bisa gayyatar Sarki Charles na III.
Idris ya ce wannan ziyara na nuna irin ƙaƙƙarfan alaƙar tarihi da ke tsakanin Nijeriya da Birtaniya, wadda ta ƙunshi hulɗar diflomasiyya, tattalin arziki, al’adu da kuma demokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa ziyarar za ta samar da damar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni masu muhimmanci da suka haɗa da kasuwanci da zuba jari, tsaro, sauyin yanayi, ilimi da kuma fasahar zamani.
Ministan ya jaddada cewa demokuraɗiyyar Nijeriya na ci gaba da ƙarfafa bayan sama da shekaru ashirin da ci gaba da mulkin farar hula tun daga shekarar 1999, tare da goyon bayan ƙarfaffun cibiyoyi, ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai masu tasiri.
Ya ce gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin tabbatar da cewa demokuraɗiyya ta kawo wa al’umma fa’ida ta ainihi ta hanyar ajandar “Renewed Hope”, wadda ke mai da hankali kan daidaita tattalin arziki, faɗaɗa damar rayuwa, ƙarfafa kariyar zamantakewa da kuma zuba jari na dogon lokaci.
Idris ya bayyana wasu manyan sauye-sauye da gwamnati ta aiwatar, ciki har da cire tallafin fetur da kuma daidaita tsarin musayar kuɗaɗen waje, waɗanda ya ce an yi su ne domin tabbatar da gaskiya a harkokin kuɗi, dorewar tattalin arziki da kuma sauƙaƙa yanayin zuba jari.
Ya ce waɗannan sauye-sauyen, tare da wasu umarnin shugaban ƙasa a ɓangaren mai da iskar gas, sun sa Nijeriya ta zama ƙasar da ta fi jan hankalin masu zuba jari a fannin mai da iskar gas a Afirka na tsawon shekaru biyu a jere, inda aka samu sama da dala biliyan takwas daga manyan kamfanonin duniya.
“A kowace dala da aka zuba jari, akwai samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya, bunƙasa ƙwarewa, farfaɗo da al’umma da kuma ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati a kowane mataki,” in ji shi.
Haka kuma, ministan ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba Nijeriya za ta ƙaddamar da wani sabon tsarin zamani na Customs Single Window, wanda zai haɗa dukkan hukumomin kasuwanci, masu shigo da kaya da masu fitar da kaya domin sauƙaƙa takardu da inganta harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
