Na daɗe da karɓar Musulunci, inji shahararriyar mai girke-girke Tayo-Osikoya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitacciyar mai tasiri a ɓangaren girke-girke a kafafen sada zumunta a Nijeriya, Tolani Tayo-Osikoya, wadda aka fi sani da “Diary of a Kitchen Loɓer,” ta bayyana cewa ta rungumi addinin Musulunci bayan ta taso a gidan Kirista. 

Wannan sanarwa ta janyo cece-kuce da martani daga mabiyanta a sassa daban-daban na duniya.

Chef T ta bayyana hakan ne a ranar 16 ga Maris, 2026 ta shafinta na Instagram, inda ta wallafa bidiyo tana bayani kan Musuluntarta da yadda ta kai ga wannan mataki.

Ta ce an haife ta cikin gidan Kirista, amma daga baya ta auri miji Musulmi, abin da ya ba ta damar fahimtar addinin Musulunci sosai.

A cewarta, shawarar da ta yanke ta sauya addini gaba zaya ta fito ne daga zuciyarta, ba tare da wani tilas ko matsin lamba daga kowa ba. Ta kuma bayyana cewa ta daɗe tana Musulma a asirce kusan shekaru goma, amma yanzu ta ji ta kai matakin da za ta iya bayyana hakan a bainar jama’a cikin kwarin gwiwa.

Chef T ta ce, sauya addini batu ne mai matuƙar sarƙaƙiya da jinƙai, amma ta tabbatar cewa ta gamsu da zaɓin da ta yi. Ta ƙara da cewa iyayenta sun amince da aurenta da miji Musulmi tun farko, sannan dangin mijinta sun karɓe ta hannu bibbiyu duk da cewa a wancan lokaci tana Kirista.

Ta bayyana cewa, shigarta Musulunci ba wani abu ne na gaggawa ba, illa wata tafiya ce ta hankali da fahimta wadda ta ɗauki lokaci. Ta ce sha’awarta ta zurfafa ilimi da fahimtar addinin ne ya jagorance ta zuwa wannan matsaya.

Da take waiwaye kan watan Ramadan na 2026, Chef T ta ce wannan shi ne karon farko da take karanta Alkur’ani gaba ɗaya da zurfin fahimta, kuma ta bayyana kwarewar a matsayin mai cike da natsuwa, gamsuwa da haske. Ta kuma ce tana ƙoƙarin cika shika-shikan Musulunci guda biyar, tare da burin sauke Farali a nan gaba.

A ƙarshe, ta jaddada cewa muhimmin abu ba wai kawai bin addini a zahiri ba ne, illa yadda mutum yake mu’amala da mutane. Ta buƙaci jama’a su riƙa tambayar kansu ko suna bin addini ne kawai ko kuwa suna ƙoƙarin kaiwa ga yardar Ubangiji da samun Aljanna.

By ukarofi