Borno: Har yanzu akwai boma-boman ƙunar baƙin-wake biyu da ba su fashe ba, inji Gwamna Zulum

Spread the love

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu da ake zargin ‘yan ƙunar baƙin-waken guda biyu da ke yawo a cikin birnin Maiduguri bayan jerin fashe-fashe da suka girgiza babban birnin jihar.

A wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Juma’a, Zulum ya ce rahotannin sirri na tsaro sun nuna cewa mutum biyar ne suka shigo cikin birnin da nufin kai hare-haren kunar bakin wake.

Ya kara da cewa daga cikin wadannan mutane, wasu sun riga sun tayar da bama-baman su, yayin da sauran biyu har yanzu ba su aiwatar da nasu harin ba, lamarin da ke kara jefa al’umma cikin fargaba.

Gwamnan ya jaddada cewa hukumomin tsaro suna bakin kokarinsu domin gano wadannan mutane tare da dakile duk wani yunkuri na kara kai hari, yana mai kira ga mazauna yankin da su kasance cikin shiri tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.

Zulum ya kuma buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suka ga yana da ban shakka, domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.

By Babaji