Jam’iyyar APC a Zamfara ta shirya karɓar Gwamna Dauda

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta bayyana cewar an kammala duk shirye shiryen karɓar Gwamna Dauda Lawal a ranar Talata Mai zuwa.

Shugaban Jam’iyyar na Jihar, Hon. Tukur Danfulani ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar yau Asabar a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau.

Hon. Tukur ya bayyana cewar jam’iyyar ta umarci Shugabannin ta na ƙananan hukumomi 14 da su shirya gangami na musamman domin karɓar Gwamna Dauda Lawal da za a gudanar a filin wasa na tunawa da Sir. Ahmadu Sardaunan Sokoto da ke a Gusau.

Hon. Tukur ya yi kira ga mambobin jam’iyyar ta APC a Jihar da su bada goyon bayan da ya dace don kammala bikin karɓar Gwamna Dauda Lawal cikin Nasara.

A cewar sa, dawowar Gwamnan cikin jam’iyyar ta APC wani gagarumin cigaba ne a Jihar.

Yayi Kira ga mambobin Jam’iyyar da su kasance masu bin doka da oda a ko yaushe .

“Jam’iyyar APC ta yi kyakkyawan shiri don karbar Gwamna Dauda Lawal da ya bar jam’iyyar sa ta PDP zuwa APC a jihar.

Blueprint ta ruwaito cewar ana saran mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shatima zai jagoranci karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar ta APC.

By ukarofi