NATO ta janye dakarunta daga Iraƙi yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙamari

Spread the love

Kungiyar tsaron ƙasashen yammacin duniya ta NATO ta janye dakarunta daga aikin horaswa da ba da shawara a ƙasar Iraki, tare da mayar da su zuwa Turai, sakamakon tsananin rikicin yaƙin Iran da ke ƙara ƙamari.

Rahotanni sun ce an kwashe dukkan jami’an NATO da ke cikin wannan aiki cikin tsaro, inda aka mayar da su zuwa wani hedikwata na soja a birnin Naples na ƙasar Italiya.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin yaƙi tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke ƙara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya haifar da fargabar tsaro ga dakarun ƙasashen waje da ke Iraki.

NATO ta bayyana cewa aikin nata a Iraki ba na yaƙi ba ne, illa dai horas da jami’an tsaron ƙasar domin ƙarfafa tsaro. Duk da janyewar, ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da hulɗa da Iraki ta wasu hanyoyi.

Haka kuma, wasu ƙasashen NATO kamar Poland, Spain da Croatia sun riga sun fara janye ko matsar da dakarunsu daga yankin, saboda ƙarin haɗarin tsaro da rikicin ya haifar.
Reuters

Masana na ganin cewa wannan janyewar na iya ƙara dagula kokarin yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a Iraki, yayin da yankin ke fuskantar sabon tashin hankali.

By Babaji