Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Wani matashin ɗan siyasa a Jihar Gombe, Zakariyya Jidda, ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai adalci da hangen nesa wanda salon mulkinsa ke ci gaba da ƙarfafa Jam’iyyar APC a jihar.
Jidda ya bayyana hakan ne yayin da yake nazari kan yadda aka gudanar da zaɓuɓɓukan cikin gida na jam’iyyar APC, inda ya ce an gudanar da su cikin lumana, tsari da kuma gaskiya ba tare da samun wani rikici ba.
A cewarsa, yadda gwamnan ke tafiyar da mulki bisa gaskiya da bin doka ne ya samar da yanayi mai kyau da ya bai wa kowa dama, wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaɓuɓɓukan cikin kwanciyar hankali daga matakin gunduma har zuwa jiha.
Ya ƙara da cewa, salon shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya ya gina amincewa a zukatan jama’a, lamarin da ke jawo hankalin ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyu zuwa APC domin su kasance cikin tsarin ci gaban da ake samu.
“Yawaitar sauya sheƙa da ake gani a yau na nuna yadda jama’a ke gamsuwa da shugabanci nagari. Mutane na shiga APC ne saboda suna ganin gaskiya da cigaba a cikin tafiyar jam’iyyar,” in ji shi.
Jidda ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su rungumi siyasa mai tsafta tare da mutunta juna, yana mai jaddada cewa haɗin kai da goyon bayan gwamnati mai aiki su ne mabuɗin ci gaban al’umma.
Ya ce lokaci ya yi da za a kauce wa saɓani mara amfani, a maida hankali kan haɗin kai domin ciyar da jihar gaba, inda ya bayyana Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin ginshiƙin haɗin kan siyasa a Gombe.
A ƙarshe, ya taya al’ummar Musulmi murnar ƙaramar Sallah, tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadu, Ya kuma ba jihar da ƙasa baki ɗaya zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
