
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, zai ziyarci jihar Zamfara domin tarbar Gwamnan jihar, Dauda Lawal cikin jam’iyyar APC a ranar Talata mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Tukur Ɗanfulani Maikatako ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Gusau ranar Asabar.
Ya ce, mataimakin shugaban ƙasar tare da shugabannin jam’iyyar na ƙasa za su halarci taron domin ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma kirayi mambobin jam’iyyar da ke gundumomi 147 na ƙananan hukumomi 14 da ke jihar da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata wajen tarbar mataimakin shugaban ƙasar da kuma nuna murna ga komawar gwamnan cikin APC.
Kazalika, ya bayyana matakin gwamnan a matsayin dabarar ƙarfafa jam’iyyar da kuma kawo ƙarshen rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yanta.
